Gwamna Nasiru El Rufa'i ya sake kebe kan sa a karo na biyu don gwajin cutar koronaGwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya sake kebe kansa daga cikin danginsa da kuma wasu manyan jami'an Gwamnatin da ke kusa da shi suka banyan tabbatar da gwajin cutar Covid-19.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wani gajeren bidiyo a shafinsa na Twitter mai suna @GovKaduna a daren Juma'a.

Tweeter din da bidiyon sun an ruwaito cewa, “an sanar da Malam Nasir @elrufai game da kyakkyawan sakamakon gwajin na Covid-19 na makusantansa, gami da danginsa na kusa da kuma manyan jami’an Gwamnatin Jihar Kaduna.

Gwamna El-Rufa'i a cikin faifan bidiyon,  ya yi kira ga jama'ar jihar Kaduna da su bi ka'idojin da aka shimfida na Covid-19, inda ya bukace su da su kasance masu wanke hannaye da sabulu da ruwan da ,sanya abin rufe fuska yayin barin gidajensu kuma su guji taro na mutane sama da shida yayin da lokacin bikin kirsimeti ke gabatowa.

Yayi alkawarin gabatar da sakamakon gwajin sa ga mutanen jihar Kaduna a ranar Lahadi.