AMISOM, sun kashe kimmanin mayakan al-Shabab 200

A wata Hira da Muryar Amurka sashin Somalia ta waya, gwamnan yankin Lower Shabelle Abdulkadir Mohamed Nur Siidi, ya ce sojojin Uganda da ke karkashin haɗakar kungiyar dakarun Afrika na AMISOM, sun kashe kimmanin mayakan al-Shabab 200 ta amfani da jirgin sama masu saukar ungulu na yaki.

Da ma da farko, mataimakin mai magana da yawun rundunar sojin ta Uganda Laftanal Kanal Deo Akiki ya ce, sojojinsu sun kashe akalla mayakan al-Shabab 189 a wani farmaki wanda  ya yi sanadiyar lalacewar wasu makamai da aka  tara. 

Gwamna Siidii ya ce hare-haren ta sama, da kuma wadanda dakarun haɗin gwiwa suka kai ta kasa, a ranar Juma’a suka faru da kuma a safiyar jiya Asabar a wasu kauyuka da ke tsakanin gundumomin Qoryoley da Janaale a kudancin yankin Lower Shabelle da ke Somalia.

“An fafata ne tsakanin  ‘yan bindigan a maɓuyar su a ƙauyukan Sigaale da Adimole da kuma Kayitoy, masu nisan kilomita 100 daga yankin kudu maso yammacin Mogadishu babban birnin Somalia,” inji Nur.

Wata sanarwa daga ma’aikatar sojin Uganda ta fada cewa, “an lalata kayan yakin soja masu dimbin yawa da ma wasu kaya da ‘yan ta’addan ke amfani da su, yayin da aka kai musu farmakin a maɓuyar tasu. 

An kuma samun Sanarwar dake cewa “dakarun UPDF na Uganda ta kuma lalata wani zaman tattaunawa da al-Shabab ke yi, inda ta raunata ‘yan ta’addan da dama a Donca-daafeedow, wanda ke da nisar  kilomita bakwai daga garin Janaale.


 VOA