Shugaban kasa Museveni na Uganda ya lashe zaɓe a karo na shida


Tun shekarar 1986 shugaban kasar Uganda Museveni yake mulkin kasar izuwa wannan lokaci inda ya kuma lashe zaben da aka fafata 

Hukumar zaben Uganda ta ayyana shugaban kasar wanda ya dade a kan mulki Yoweri Museveni a matsayin wanda ya lashe zaben kasar, sai dai kuma babban abokin hamayyarsa Bobi Wine ya yi zargin an tafka mummunar magudi a zaben. 

Mr Museveni ya lashe kusan kashi 59 na kuri'un da aka kada, yayin da shi abokin karawar nasa Mr Wine ke bi masa da kashi 35, a cewar Hukumar zaben.

Mr Wine, wanda tsohon mawaki ne, ya kalubalanci rashin sahihancin zabe tun da farko,  kuma ya yi alkawarin gabatar da shaidun da ke nuna cewa an tafka magudi. 

Sai dai Hukumar zaben ta musanta cewa an yi magudi a zaben wanda ya gudana a ranar Alhamis din nan da ta shude. 

Masu sanya ido a zaben sun soki gwamnati bisa toshe shafukan sadarwa ta intanet don cimma wani buri da suke da ita. Sun ce hakan ya nuna cewa zaben ba shi da sahihanci. 

Mr Wine ya ce zai gabatar da shaidun sa da zasu tabbatar da cewa an  tafka magudin zabe da zarar an sake bude hanyar intanet.

 Mutane da dama ne suka rasa rayukansu sakamakon rikicin da ya barke gabanin zaben. 'Yan jam'iyyun hamayya sun zargi gwamnati da cin zarafinsu.

Wannan Sakamakon zaben zai bai wa Shugaba Museveni damar yin mulki a wa'adi na shida a kasar ta uganda.

Shugaban kasar mai shekara 76 - wanda ya hau kan mulki a 1986 - ya ce bashi da wani kudiri da ya wuce tabbatar da kwanciyar hankali da ci gaba a kasar.

A nasa bangaren, Bobi Wine - mai shekara 38 wanda sunansa Robert Kyagulanyi - ya ce ya samu goyon bayan matasa a daya daga cikin kasashen da ke da mafi yawan matasa a duniya.

Ranar Juma'a, a yayin da ake fitar da sakamakon zaben, Mr Wine ya ce gwamnati tayi amfani da sojojin kasar ta Uganda sun yi wa gidansa ƙawanya sannan daga bisani suka yi masa kutse.

Sai dai mai magana da yawun gwamnatin ƙasar ya zargi  Mr.  Bobi Wine mayar da batun kamar wani wasan kwaikwayo domin ya sa a ji tausayinsa.

Shugaban hukumar zaben mai Sharia'a Simon Mugenyi Byabakama ya  ayyana Yoweri Museveni... a matsayin zababben shugaban kasar Uganda a ranar Asabar. 

Ya kara da cewa kashi 57 na masu kada kuri'a ne suka yi zabe wato kusan mutum miliyan 18 da suka yi rijistar zabe. 

Mr Byabakama ya ce an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, sannan ya yi kira ga Mr. Bobi Wine, wanda ya ke cewa an kama wasu jami'an kula da zabensa a ranar Alhamis, da ya gabatar da shaidun sa kan zargin da ya yi na tafka magudi.

Anyi fama da rikicin zabe wanda ba a taba ganin irin sa ba gabanin zaben kasar, kuma mutane da dama sun mutu sanadin dirar mikiyar da jami'an tsaro suka rika yi musu.

Gwamnati ta ce ta haramta taron jama'a domin hana yaduwar cutar korona amma 'yan hamayya sun ce an yi hakan ne da zummar murkushe izzar da suke da ita na samun nasara a zaben. 

Bbc