Ƙungiyar yarabawa sun gargaɗi ƴan arewa su sassauta kalaman su ka rikicin su da makiyaya


Ƙungiyar Yarbawa mai lakabi da Afenifere dake kudu maso yammacin najeriya ta gargadi kunnen ƙungiyar tuntuɓa ta Arewacin Najeriya game da yin dukkan wasu kalamai da za su zamo goyon baya ga makiyaya da aka bai wa wa'adin ficewa daga wasu sassan jihohin kudu maso yammacin najeriyar.

Ita dai ƙungiyar tuntuɓa ta arewacin ƙasara ta yi gargaɗin cewa kokarin korar makiyaya daga wani yanki na kasar da kuma harin da aka kai musu kwanan nan a jihar Oyo, na iya kawo barazana ga zaman lafiyar ƙasara kasancewar irin ƙalubalen da ƙasar ke fama da shi ta harkar tsaro. 

Sai dai cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta Afenifere ta Yarbawa ta fitar, ta ce dole ne al'ummarsu ta kare kanta daga abin da ta kira "wasu da suka fi fifita shanunsu fiye da dan adam".

Afenifere ta ce masu barazana da yaƙin basasa su kwana da sanin cewa al'ummarta ba kanwar lasa ba ce, don haka ba za ta naɗe ƙafa tana kallo a ci gaba da kisan jama'ar yankin su ba.

Sai dai masana a harka tsaro kamar su Barista Audu Bulama Bukarti yayi kira ga gwamnatin tarraya da ta ɗauki matakan da suka dace kan lamarin tsaro a fadin ƙasar baki daya don gujewa afkawa cikin mummunar matsalar da zata hana kasar cigaba ta kowane fanni. 

Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredulu ne ya fara bai wa makiyaya a jiharsa wa'adin mako guda domin su fice daga cikin dazukan jihar, lamarin da ya janyo martani daga gwamnatin tarayya ta Shugaba Muhammadu Buhari.

Wanda ke ƙunshe cikin rahoton da muka kawo muku a makwan jiya.