A daren jiya juma'a Gobara ta hallaka kimanin shaguna 100 da duniyoyi a kasuwar wunti Bauchi


Matsananciyar gobara  ta tashi  a daren jiya Juma'a ta lashe  shaguna kimanin guda100 a Kasuwar Wunti da ke birnin Bauchi na Jihar Bauchi hakazalika babu Wanda har yanzu ya san dalilin tashin wutarc

Majiyar mu sun shaida mana cewa wutar ta tashi ne tun misalin ƙarfe 12:00 a ɓangaren da ake masu gyaran  kwamfutoci da shagunan teloli da na masu gyaran gashi.

ko da yake al'amarin ya faru cikin dare ne sosai ba a samu asarar rai ba, sai dai 'yan kasuwa sun yi asarar dukiya mai ɗimbin yawa wanda har yanzu ba a kai ga tantance adadin su ba.

Gwamnan  Bala Mohammed ƙaura na jihar Bauchi ya kai ziyara kasuwar domin ganewa idonsa abinda ya faru kana ya  jajentawa 'yan kasuwan da wannan iftila'i ya afka Musa.

Har zuwa wayewar gari yau asabar da akwai wasu sassan da ke ci da wuta wanda hakan ya sa duk harkokin kasuwanci suka tsaya cak a kasuwar a yau Asabar.

Yahuza Haruna Bauchi