A Daren Jiya juma'a Kimanin ɗalibai Mata 300 ne Ƴan bindiga suka sace a GSS Jangebe ta jihar Zamfara

 

Rahoto daga Zamfara dake Arewa maso Yammacin Najeriya na tabbatar Cewa wasu Ƴan bindiga sun sake sace kimanin dalibai mata 300 daga Makarantar Sakandaren GSS Jangebe da ke jihar Zamfara da tsakar dare a ranar Juma’a jiya

Mahaifin daya daga cikin daliban da kuma ɗaya malami daga cikin malaman makarantar sun tabbatar wa wakilin manema labarai faruwar lamarin.

Har zuwa yanzu dai rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara da kuma gwamnatin jihar ta Zamfara ba su ce komai game da faruwar lamarin ba.

Wanda a halin da ake ciki ana  cigaba da kokarin kubutar da daliban Makarantar Sakandare da Kungiyar Malaman su da wasu ƴan bindigan suka sace makwan Jiya a jihar Neja.

Cikakken rahoto kan lamarin na nan zuwa muku da zarar mun kammala haɗawa.