A na dab da sanar da sakamakon zaben shugaban ƙasar Nijar zagaye na biyu.

Sakamakon zaɓen Jamhuriyar Nijar zagaye na biyu da ya gabata a a cikin makon jiya alamu sun nuna cewa Bazoum Mohamed na jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki na dab da lashe zaɓen.

Hukumar zabe mai zaman kanta CENI yanzu haka ta fara  fitarwa ya  sun nuna cewa Bazoum ne yake da sama da kuri'a miliyan 2 da dubu 500. na ƙuri'un da aka naɗa.

Dan takarar jam'iyyar RDR Tchanji Mahamane Ousmane ya samu kuri'a sama da miliyan 1 da dubu 800 cikin ƙuri'un da aka naɗa.

Wakiliyar BBC da ke Niamey Tchima Illa Issoufou ta sanar da cewa hukumar zaben ta CENI ta wallafa sakamakon gundumomi 259 daga cikin 266 wanda ke nan a na daf da kamala aikin fitar da sakamakon zaben.

Sai dai mataimakin shugaban hukumar CENI Dr Aladoua Amada ya tabbatar wa manema labarai cewa duk da yake saura sakamakon gundumomi 7 amma ba za su iya canja akalar sakamakon ba kasancewar a zagayen farko na zaben shugaban kasa  Bazoum ne ya lashe zaben.

Hukumar zaben ta ce ana sa ran yau Talata da misalin karfe 11 na safiya ne za'a sanar da sakamakon wucingadi na zaben.