Alamomi na nuna cewa Tsohon shugaba Jonathan da El-Rufa'i na shirin zama shugaban ƙasa a jam'iyyar APC 2023


Ƴan Najeriya da dama na ganin cewa bai kamata tsohon Shugaban Ƙasar Goodluck Ebele Jonathan ya sake tsayawa takarar kujerar shugaban ƙasa ba, yayin da ake ci gaba da raɗe-raɗin cewa jam'iyyar APC mai mulki na zawarcin sa don za ta tsayar da shi a zaɓen 2023 mai zuwa.

A safiyar Litinin ɗin nan ne aka sake sabunta wannan jita-jitar cewa jam'iyyar APC  na shirin tsayar da Jonathan ɗin a matsayin ɗan takararta a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa tare da Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai a matsayin mataimaki koda yake wannan labari ya kewaye kafafen yaɗa labarai na duniya.

Sai dai har zuwa yanzu daga shi Jonathan da APC harma da shi Nasir El-Rufai, da dukkan waɗanda abin ya shafa, babu wanda ya ce komai game da labarin, amma kamar yadda dai aka saba ƴan Najeriya sun yi ta amfani da shafukan sada zumunta domin goyon baya ko akasin haka.

Idan baku manta ba a kwanakin baya cikin wata hira da BBC  shugaban jam'iyyar APC na riƙo a matakin ƙasa, Gwamna Mai Mala Buni ya Musanta zargin cewa suna shirin tsayar da tsohon Shugaban takara.

Saidai wasu manazarta al'amurra suna ganin cewa babu shakka akwai yiwuwar ƙamshin gaskiya a batun dake neman kasance duk mako sai an sabunta shi.