Ban yarda ku ci mutumcin Wani ba saboda ni. cewar Hon Ahmad Aliyu Wadada, yayin sabanta katin jam'iyya.


A cigaba da aikin sabanta katin kasancewa cikakken ɗan jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya daya daga cikin manyan zaratan ƴan siyasar jihar Nassarawa Hon. Ahmed Aliyu Wadada (Sarkin Yaƙin Keffi).

A yau Alhamis ya ziyarci mazaunan a garin Keffi don sabanta katin sa, sai dai wani babban abinda yafi damar hankalin al'umma shine irin tawagar da suka yi gangami domin raka shi yankar katin.

Taron dafifin jama'an sun haɗu ne a mazabar sa kana wakilai daga shiyoyi daban-daban sukai ta tofa albarkacin bakinsu game da Sarkin Yaki.

Cikin jawabin nasu sunyi ta nunawa Hon.A. A Wadada goyon bayan su gare shi tare da kiraye kiraye don ya tsaya takarar kujerar sanata a shekarar 2023.

wanda suke tabbatar masa da cewa wannan hanyar ce kaɗai zasu iya rama masa karanci da hidima da yake yi musu.

A cikin jawabin sa na nagodiya ga mahalarta taron musamman matasa ya jawo hankalin su da su daina cin mutuncin Kowa yayin da suke yabawa ƙoƙarin sa a siyasance. 

Hakazalika ya ƙara da jan hankalin al'umma da su tabbatar su fito don sabanta katin kasancewa cikakkun ƴan jam'iyyar APC domin tunkarar dukkan Wani kalubale da ka Iya tasowa yayin zaɓen fidda gwani.

Murjanatu Z. Ajiya