Ci gaban Tarihin Marigayi Sir Ahmadu Bello Sardaunan kashi na biyu 2

                Gamji ƊanƘwarai

Kamar yadda muka fara kawo muku Tarihin Marigayi Sir Ahmadu Bello Yau zamu ci gaba 

A shekara ta 1948, sir Ahmadu Bello ya kai ziyarar aiki Ingila inda ya sauka a gidan abokan sa kuma suka zagaya da shi kasar, ya kuma zauna da su yana halartar kwas akan mulkin kanan hukumomi.

A shekara ta 1949 marigayi sarduna ya sami zuwa majalisar dokoki ta jihar arewa,yana kuma daga cikin mutum na uku da aka zaba cikin kwamitin da ya rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasa.

An nada shi firimiyan Najeriya ta arewa a shekarar 1954. Ya riki wannan mukami har tsawon shekaru goma-sha-daya, Daga bisani  aka kashe shi a yunkirin juyin mulkin soja na farko a kasar ta Najeriya.

Kashe Sir Ahmadu Bello Sardaunan wanda  Allah yayiwa baiwa ta basira da tunani al'ummar sa da kuma hangen nesa,  kasheshin da aka yi a ranar 15 ga watan janairun 1966 a yunkurin juyin mulkin soja na farko a Najeriya, shine ya kawo karshen tsarin mulkin jamhuriya ta farko a wannan kasa ta Najeriya.

Sojan da ya kashe shi kuwa ya haska Fitina ne don ya gane sardauna, a lokacin Sardaunan na kalonsa ya harbe shi har lahira, ya kuma harbe uwargidansa da suke tare Habsatu,

koda yake an harbe Sardaunan amman kuma duk da haka yana tsaye bai fadi ba, jikinsa duk jini,a wanan lokacin ne kuma sallam ta taba shi, ya gane cewa Sardaunan ya gamu da ajalinsa,

Ba’a dai taba sauran matayen Marigayi sardauna ba, in banda ita uwarginsa da aka harbe su tare.

Sardauna yasan cewa za’a yi juyin mulki a wanan daren,don haka ne ya umarci kowa ya bar gidan da suke zaune a birnin Kaduna wanda gidan gwamnatin arewa yake.

Tarihi ya nuna cewa Alh. Aliyu magajin garin Sakkwato ne ya sanarda sarkin musulmi rasuwar sardauna wanda daga bisani ne sarkin musulmi ya yarda a yi jana’izarsa tare da matarsa Hafsatu Kamar yadda addini ta tanada.

Yayi  jana'idar sa, Marigayi shiekh Abubakar Gumi ne ya shugabanci Sallar jana’izar Marigayi Sardauna Sir Ahmadu Bello.

Ga mai buƙatar Sanin fiye da abin da muka ambata Ku ziyarci gidan tarihin Sakkwato hatta rigar sa da aka harbe shi Yaman don inganta tarihi har ma da wasu ababe tarihi game da shi.