Cristiano Ronaldo ya sayi Motar £ miliyan 8 don murnar zagayowar ranar haihuwarsa inda yake cika shekaru 36


Don murnar zagayowar ranar haihuwarsa yayin da yake cika shekaru 36, Cristiano Ronaldo ya sayi mafi girman Mota samfurin  Bugatti Centodieci kimanin £8- miliyan motar da za ta iya tafiya mai nisan gaske aƙanƙanin lokaci.

Dan wasan na Juventus yana da tarin tarin motocin samfurin Buga ttun. da dama wanda ya ajiye a gidansa dake ƙasar Italiya.

A iya cewa shedar wannan ɗan wasa Ronaldo, abokin ciniki ne na yau da kullun na motocin Bugatti, ya sayi Veyron, da Chiron da kuma La Voiture Noire - inda daga baya aka mayar masa da dala miliyan 18 a bara.

Ya kuma mallaki Ferrari F430, da Phantom Rolls-Royce, da Lamborghini Aventador da kuma mashahurin Maserati GranCabrio.

Twitter