Dan wasan gefe na Chelsea da Moroko Hakim Ziyech mai kimanin shekara 27, na tunani kan makomar sa

Ga dukkan alama dan wasan tsakiya na Burnley ɗan Kasar Ireland Robbie Brady, mai shekara 29 na iya komawa Celtic ta ƙasar Spain a kakar wasa ta bana.

Mai horar da ƴanwasan Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce har yanzu yana sa ido kandan wasan gaba Erling Braut Haaland na Borussia Dortmund da Norway mai shekara 20 duk da cewa  kungiyar ta kasa dauko shi a bara.


Arsene Wengert tsohonkocin Arsenal   ya ce ya yi dukka mai yiwuwa domin sayen Jamie Vardy, dan wasan gaba na Leicester City mai shekara 34 a 2016 abin yaci tura. 

Ƙungiyar Atletico Madrid  da Juventus da Paris St-Germain na  daga cikin manyan kungiyoyin da ke sha'awar raba Ɗan wasa Renato Tapia da kungiyarsa ta Celta Vigo a kakar wasan bana.

Kocin Chelsea Thomas Tuchel ya gargadi matasan ƴan kwallo na kungiyar da su shirya samu kalubale da tafiya wasu kungiyoyin a matsayin ƴan aro domin su nuna ƙwarewar su.

Dan wasan gefe na Chelsea da Moroko Hakim Ziyech mai kimanin shekara 27, na tunani kan  makomar sa  bayan da ya kasa burgewa bayan ya baro Ajax

Sports News