Dokar saka takunkumin rufe baki ya fara aiki a Najeriya


A cikin makon jiya ne gwamnatin Najeriya ta tabbatar da dokar saka takunkumi rufe baki don rigakafin kamuwa da cutar koronan.

Dokar Wanda nan take ta fara aiki a Najeriya musamman a cikin babban birnin kasar Wato a Abuja.

Watata kotun tafi da gidanka a Najeriya ta yankewa mutum fiye da 100 waɗanda suka karya ka'idojin dokar kariya daga cutar korona hukuncin biyan tara a Abuja.

Wanda tun daga lokacin da aka kafa dokar aka sanar da cewa akwai tara Ko hukunci daurin watannin shida.

Kotun ta yankewa mutanen ne hukunci bayan ta same su da laifin ƙin sanya takunkumi a cikin jama'a kamar yadda dokar ta tanada.

Rahoton. Rilwan Zubairu