Guguwar sauyi na kasuwancin 'yan kwallo ya kwaso su;- Haaland, Alaba, Mo Salah, Mbappe, Upamecano, Sule, Lingard
A na kyautata zaton Mo Salah, dan wasan gaba mai shekara 28 ne zai bar Liverpool da zarar ƙungiyar ta dauko Kylian Mbappe dan wasan gaba mai shekara 22 daga Paris St-Germain.
Kungiyar Manchester City ta kasar na ganin dan wasan gaba na Borussia Dortmund Erling Braut Haaland mai shekara 20 zai amince da komawa ƙungiyar idan ta nasarar lashe gasar firimiyar Ingila a bana.
Ƙungiyar Chelsea ta sha alwashin shan gaban Real Madrid wajen daukan dan wasan baya na Bayern Munich da Austria David Alaba, mai shekara 28.
Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce Paul Pogba, dan wasan gaba na kungiyar mai shekara 27 ya tabbatar da a shirye yake ya tsawaita zamansa kwantiragin sa a ƙungiyar dake Old Trafford . (Bbc)