Gwamna Umar Gandije Ya tsige Salihu Tanko Yakasai kan batun nuna gazawar Gwamnatin Buhari da APC akan Matsalar tsaro


Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya tuɓe Salihu Tanko Yakasai daga muƙamin na mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai bayan ya soki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da cewa sun gaza a harkar tsaro

A jiya Juma'a ne Salihu Tanko Yakasai, wanda aka fi sani da Ɗawisu a shafukan zumunta, ya yi kira ga gwamnatin jam'iyyar APC ƙarƙashin shugabancin Shugaba Buhari da ta "kawo ƙarshen matsalolin tsaro ko kuma su sauka daga mulk.

Wanda yace kasa kawo karshen ayyukan ta'addacin da sace-sacen mutane da ƴan bindiga ke yi a ƙasa alama e da ke nuna gazawar Gwamnati a sha'anin shugabanci

Wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai Mohammed Garba ya fitar ya tabbatar da cewa gwamnan ya ɗauki matakin ne saboda "kalaman rashin kan gado" yayi a cewar sa  

Sanarwan ta soki Salihu da cewa ya kasa tantancewa tsakanin ra'ayi da na ƙashin kansa da kuma ra'ayin gwamnati kan abubuwan da suka shafi al'umma, saboda haka ba za a bar shi ya ci gaba da aiki tare da gwamnatin da ba ya goyon baya ba Mohammed Garba ya sanar da cewa dakatarwan ta fara aiki ne nan take.

BBC Hausa