Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya bada Ummurnin rufe dukkan Makarantun kwana na Jihar

Biyo bayan Mummunar al'amarin da ya faru na awon gaba da 'yan bindiga sukayi da dalibai da maluman su a makaratar sakandaran gwamnati dake kagara cikin jihar Neja Gwamnatin jihar  Neja ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun kwana da ke fadin  jihar.

Sanarwar ta fito ne daga Gwamnan jihar Abubakar Sani Bello  ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Tuwita a safiyar Laraban nan makarantun da za'a rufen sun hada da Makarantar kwana ta Rafi,Munya, shiroro harda karamar hukumar Mariga.

A cewarsa: "Gwamnatin jihar Neja ta bayar da wannan umarnin na  rufe dukkan makarantun kwana nan take a kananan hukumomin da suka zaiyano sakamakon matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a fadin kasar nan

'Yan bindiga na ci gaba da dauke 'yan makarantu a sassasan kasanan, ci gaba da garkuwa da mutane da suke yi musamman araewacin Najeriya al'amarin na dada ta'azzara mahukunta da mazauna yankunan da abin fi tsananta,

A cikin  watan Disambar bara an sace dalibai fiye da 300 daga makarantar sakandaren a garin  Kankara da ke jihar Katsina lamarin da ya ja hankalin duniya.

Twitter