Jam'iyar APC na shirin baiwa Tsohon shugaban ƙasa Jonathan Tikitin takara a 2023

Masana harkokin siyasa a Najeriya sun fara tofa albarkacin bakinsu a kan zancen da a ke cewa jam`iyyar APC mai mulki na zawarcin tsohon shugaban najeriyar  Goodluck Jonathan domin ya tsaya takarar shugabancin ƙasa a karkashin tutart jam'iyyar a ta APC a zaɓen mai zuwa na shekarar 2023.

A wasu rahoton bayan ganawa da wasu gwamononi daga arewacin kasar ne ke matsawa wajen ganin hakan ta tabbata, inda suka bayar da hujjar cewa saboda wa`adi ɗaya kawai tsohon shugaban ƙasar zai yi, sai mulki ya sake komawa yankin arewacin ƙasar.

Sai dai masana harkokin  siyasar ƙasar na cewa hakan alama ce da ke nuna rashin aƙida da rashin ƙwarewar siyasa a tsakanin ƴan siyasa masanman ƴan jam'iyyar ta APC mai mulkin ƙasar. 

Masanan na ganin cewa wasu manyan jam`iyyar sun gwammace dawowar tsohon shugaban ƙasa Jonathan ne ya kasance magajin shugaba Buhari, saboda ba zai tsananta bincike da yi musu bi-ta-dakulli ba, bayan haka ma zai fi daɗin tafiya a kan wanda zai fito daga wata shiyya ta daban, ko daga shiyyar kudu maso yammaci ko kudu maso gabashin kasar, 

sannan kuma koda ya hau kujerar ba zai wuce wa`adi daya ba, kuma bayan hakan sai mulki ya kuma dawowa ga 'yan arewa ganin cewa tun a baya ya yi wa'adi guda ne kafin gwamnatin shugaba buhari ta kawar da shi kimanin shekaru biyar da suka shuɗe. 

Dr Abubakar Kari, kwararren malami ne a jami`ar babban birnin tarraya da ke Abuja ya furta cewa Wannan na nuna cewa a siyasar Najeriya babu aƙida babu alƙibila, hakan ta sa ake yiwa siyasa kwasan karan mahaukaciya kuma komi ya na iya faruwa.

A cewar Dr. Kari Idan ba haka ba Goodluck Jonathan wanda a baya aka taru baki daya aka ce ya gaza ya kasa a zamanin mulkin sa ya yi rauni kwarai da rashin gaske kuma a ce shi ne yanzu za a ruka zauwarcin sa ya dawo ya sake mulkin kasar.

haka kuma masanin ya kara nanata cewa: ''Irin wannan komen ba alheri ba ne ga ƙasa kamar Najeriya.''

Zuwa yanzu dai, babu wani bayani daga uwar jam`iyyar APC ta ƙasa  mai mulki da aka ce ta na neman zawarcin tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan don ya mata takara a zaɓe mai zuwa na 2023.

haka dai shima ɗaya ƙari har daga bangaren tsohon shugaban ƙasar babu wani da ya fito ya ɗaga yatsa domin musunta wannan maganar.

To amma ta wani ɓangare wasu ƴaƴan jam`iyyar ta APC na cewa rungumar tsohon shugaban kasar babban kuskure ne ga jama'ar ta APC. da ma alummar kasan

Alhaji Ibrahim Masari, jigo ne a jam'iyyar ta APC mai mulki na cewa:' ''Yin haka ya kasance tamkar renawa talakan Najeriya hankali da wayo ne, 

multumin da jam'iyyar APC ta yi wa zarge -zarge masu yawa bila-adda-din, na tsawon shekaru takwas a ce yau ya dawo ya yi takara ƙarƙashin wannan jam'iyar, wanda hakan  na nufin cewa dukan mu ƴaƴan jam'iyar APC da magoya bayanta sun yi karya? ko kuma sake rikiɗa ya yi ?