Kasar Nijar Na fafatawa a Zagaye na biyu a zaben Shugaban kasarA yau lahadine 'yan takara biyu suke fafatawa karo na a zaɓen da Mohammmed Bazoum na jam`iyyar PNDS Tarayya mai mulki, da kuma Mahaman Ousman na babbar jam`iyyar adawa ta RDR Tchanji. A zagayen farko na zaɓen ɗan takara Mohammmed Bazoum na jam'iyya mai mulki ya samu rinjaye da kashi 39.3 yayin da tsohon shugaba Mahamane Ousmane yake da kashi 16.9 cikin ɗari wanda hakan yake nuna Bazoum ke gaba a wancan karon.

kuri'un da ya samu alama ce dake nuna yana da magoya baya a cikin al'ummar hakazalika Bazoum yana da goyon bayan ƴan takarar da suka zo na uku da na huɗu a zagayen farko na zaɓen, shi kuma Ousmane yana sa ran samun goyon baya daga gamayyar jam'iyyun hamayya 18 a wannan  karon.

Daga Bangaren adawa sun yi tur da zargin maguɗin zaɓe, sannan ya ce ba zai yarda da sakamakon zaben  zagaye na biyu ba matuƙar sun lura an tafka maguɗi a zaben dake gudana.

wannan Zaben na yau shi ne karon farko da za a miƙa da kuma karɓar mulki cikin lumana tsakanin shugabannin da aka zaɓa ƙarƙashin tsarin dimokraɗiyya a ƙasar ta Nijar da siyasarta ke tangal-tangal.

Nijar dai ta fuskanci juyin mulki sau huɗu a hannun Faransa cikin 1960. Ana sa ran samun sakamakon zaben na wucen gadi cikin kwanaki biyar masu zuwa bayan kammala zaben na yau,