Kasar Somalia da ke cika shekaru talatin da rushewar mulkin kama karya,Na shirin Zabe

Kasar Somalia da ke cika shekaru talatin da rushewar mulkin kama karya a kasar da ke fama da rikice rikice da suka addabi kasar, gwamnatin ta shirya gudanar da zaben kasar mai cike da rikici.


Wasu  daga jihohin kasar biyu sun ki shiga zaben na shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar ts Somalia, yayin da lokacin da aka kayyade a ranar takwas ga watan Janairu wannan shekarar ya ke karatowa.

Dokar majalisa ta baiwa shugaban kasa Mohamed Abdullahi Mohamed da ‘yan majalisar dokokin kasar su ci gaba da aiki, amma idan suka haura ranar takwas ga Faburairu, akwai yiwuwar fadawa cikin wani mummunar rikicin siyasa a kasar wanda ba a bukatar ji ko ganinn irin wannan tarzoma, inji wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman James Swan, ya fadi hakan a wannan makon da ake ciki.

A cikin kafa allunar gangamin neman zabe da yin jawabai a babban birnin kasar, Mogadishu akwai alamun damuwa a birnin, yayin da ake kira ga mutane su marawa ‘yan takaran baya amma kuma ba zasu iya yin hakan kai tsaye ba.

Zaman tankiya da ake yi a kasar ka iya baiwa kungiyar ta’addancin Somalia ta al-Shabab damar kai hare hare,ta ko ina  a kasar wacce a baya ta yi barazanar kai hari a runfunar zabe.. A hali da ake ciki, yanzu ne kuma kasar take kokarin cike gurbin sojojin Amurka 700 da aka janye su, wani aiki da aka kammala a cikin watan Janairu.

Samun nasarar gudanar da zaben cikin lumana na nufin gwamnatin Somalia zata iya maida hankali wurin daukar matakan gaggawa a kan batutuwa kamar annobar COVID-19 da farin dango da kuma batun canjin yanayi da fari da suka shafi dubban dubatar mutane.


BBC