Makomar ƴan wasan ƙwallon ƙafan a ƙungiyoyin su a kakar wasan Bana

Chelsea na kara samun karfin gwuiwar sayen Erling Braut Haaland, dan wasan gaba na Norway mai shekara 20 daga Ƙungiyar Borussia Dortmund. 

Dan wasan gaba na Juventus  Paul Dubawa ɗan ƙasar Argentina Paulo  mai shekara 27 yana  shirin barin kungiyar sa domin akwai batun sayar da shi a karshen kakar wasan bana.Cikin kungiyoyin da ke bukatar Dybala akwai Liverpool, Manchester United da Tottenham ƴan ƙasar Ingila.

Ƙungiyar Tottenham da ta Borussia Dortmund sune kan gaba wajen kokarin dauke ɗan wasan Manchester Dean Henderson daga, Manchester United. Henderson shi ne golan United mai shekara 23.