Mohammed Bazoum ya lashe zaben shugaban ƙasar Nijar zagaye na biyu.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa Bazoum Mohamed na jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulkin ƙasar shi ne ya lashe zagaye na biyu na zaben da aka gudanar a  ranar Lahadin da ta gabata.

Alkaluman da hukumar zaben ta CENI ta fitar dazun nan sun nuna cewa Bazoum ya samu sama da kuri'a miliyan 2 da dubu 501na ƙuri'un da aka naɗa.

Dan takarar jam'iyyar RDR Tchanji Mahamane Ousmane, wanda yake biye masa, ya samu ƙuri'a sama da miliyan 1 da dubu 968.

Wakiliyar BBC da ke Niamey Tchima Illa Issoufou ta ce hukumar zaben ta CENI ta sanar da sakamakon dukkan gundumomi 266 wanda ya tabbatar wa da Mohammed Bazoum nasarar zama shugaban kasar Nijar.