Nijeriya ta kaddamar da Kamfanin Stallion Motors kamfanin Hyundai-Kona, mota mai amfani da wutar lantarki 100% a Najeriya


An yi nasarar kaddamar da mota kirar Hyundai-Kona" mai amfani da lantarki a Najeriya nan bada jimawa ba zai kasance a titunan Najeriya. 

Wannan motar lantarki ta 100% an haɗa ta akanfanin Stallion Motors. Za'a sanya wannan samfurin a kasuwannin Najeriya kafin karshen shekarar 202i, a cewar kamfanin motoci na Najeriya.

 Gabatarwar "Hyundia-Kona" ta zo ne a cikin wani yanayi na musamman a Najeriya. Wanda yawancin kasar Afirka ta Yamma take son rage hayakin da yake gurɓata yanayi.

gwamnatin Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tare da Volkswagen don gina kamfanin hada mota a kasar. 

Har ila yau, kawancen ya shafi kirkirar makarantar horaswa tare da hadin gwiwar gwamnatin Jamus da kuma "fadada" horo na fasaha na al'umma a fagen fasahar kera motoci.

Samarda wannan Mota kirar Hyundai-Kona da ke amfani da lantarki zai matukar taimaka wajen rage yawan kuɗaɗen da ake kashewa wajen sayan man fetur.

Shuraihu Usman