Ronaldo da Messi suna kan hanyar komawa Amirka da wasan kwallon su

Ƙungiyar Bayern Munich ta yi tayin sayen dan wasa  Kalidou Koulibaly, ɗan ƙasar Senegal mai shekara 29 daga ƙungiyar Napoli kan kuɗi fam miliyan 39

Shugaban bangarar horaswa da ƴanwasa na AC Milan Paolo Maldini na son tataunawa da Chelsea kan mayar da Fikayo Tomori, dan wasan kungiyar mai shekara 23 kuma dan Ingila ya zama dan wasansu na din-din-din. 

Real Madrid ta ƙasar "Spain" ta bi sahun sauran ƙungiyoyi irin su Manchester City da Juventus wajen neman sa'ar dauke Manuel Locatelli daga Sassuolo, dan wasan tsakiya na Italiya mai shekara 23.

Mai kungiyar Inter Miami David Beckham ya ce "yana da niyyar" kai 'yan wasa kamar Lionel Messi, dan wasan Barcelona mai shekara 33 da Cristiano Ronaldo na Juventus mai shekara 36 zuwa kungiyar ta kasar Amurka .

Koci Jurgen Klopp na Liverpool ya yabawa ɗan wasa  Mohamed Salah da cewa ɗan wasa ne mai matukar muhimmanci a kungiyar kuma yana fatan mai shekara 28 ɗin zai ci gaba da rike wannan mukamin na lokaci mai tsawo.