Saudiyya ta Rufe Masallatai Goma 10 na wuccin gadi kasancewar an samu Masu koronan


Ma'aikatar addinin musulunci ta  ƙasar Saudiyya ta sanar da rufe masallatai 10 a larduna 6 na wucin gadi bayan an samun wasu masu sallah a masallatan da cutar korona.

Lardunan sun hada da Jizan, Riyadh, Makkah, Adir, Madina da yankin gabashin kasar.

Zuwa yanzu an bude uku daga masallatan a Riyadh da yankin gabashi bayan gudanar da feshin magani.

A kwanakin nan Saudiyya ta rufe masallatai 135 don kalubalen korona inda daga bisani bayan kammala fesa magani a ka bude 108 a cikin su.

Ma'aikatar ta ce za ta cigaba da binciken masallatai a fadin kasar don tabbatar da kare masu ibada daga cutar ta annobar koronan.

Daga Yahaya Turba