Shugaban ƙasa ya aike da Tawagar jami'an tsaron Najeriya sun isa Neja don ceto ɗaliban da aka sace

Kimanin ɗalibai 27 ne aka sace da ma'aikata guda 12 har da iyalansu sanarwar ta fito ne daga gwamnatin jihar Neja

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce ya samu labarin wannan mummunan al'amari na sace daliban  makarantar sakandaren Kagara,  shugaban kasa ya sha alwashin ceto dalibai da sauran mutanen  daga hannun 'yan bindigar.

A sanarwar da Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya aike wa manema labarai, cewa "bayan samun wadannan rahotanni, Shugaban kasa ya umarci dakarun soji da na ƴan sanda su tabbatar sun  ceto dukkan wadanda aka sace ba tare da an yi musu lahani ba."

"Kazalika Shugaban kasa ya aike da tawagar manyan jami'an tsaron Najeriya  zuwa Minna da ke jihar Neja domin sanya hannu kan aikin ceto. 

Sannan su gana da jami'an gwamnatin jihar da shugabannin al'umma da iyaye da kuma malaman makarantar, cewar Garba Shehu.

Hakazalika Shugaban ya ce yana yin fata ganin an ceto an ɗaliban da aka sace, kana ya yi tur da Alkawarin da irin wannan ayyukan ta'addacin harin  kan daliban da ba su ji ba ba su gani ba.

Ƴan bindiga na matsa kaimi wajen kai hare-haren ta'addanci  kan ɗaliban makarantu a ci gaba da garkuwa da mutane da suke yi musamman a arewacin Najeriya Wanda hakan yana jefa tsoro a zukatan al'umma mazauna yankunan.