Shugaban Majalisar Najeriya Ahmad Lawal Yace: Gwamnonin jihohin kudancin kasan nan kalamansu ya taimaka waje ruruta wutar fitinan abun da ya faru a Oyo injiShugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Ahmad Lawan, ya ce dole ne sai an hukunta waɗanda suka kashe mutane yayin rikicin da yafaru a'yan kwanakin bayan  nan da aka samu tsakanin Hausawa da 'Yan kabilar Yarbawa a jihar Oyo.

Yayin wata hira da shugaban majalisar dattawan Najeriya yayi da gidan radiyon  BBC Ahmad Lawan ya ce baya ga biyan diyyar rayukan da aka kashe da gwamnatin jihar ta lashi takobin zata biya,  ya kamata a tsananta bincike don gano waɗanda suka haifar da wannan tashin hankalin a kuma gurfanar da su a gaban kotu, domin a yi musu hukunci dai dai da abin da suka shuka.

Abin da ya faru a jihar  Oyo da kuma wasu jihohin kudancin kasan nan an samu rashin shugabanci a cewar sanata Lawal, ba zan ce na gwamnoni kaɗai ba, amma dai su suke da muhimmin haƙƙi na kare mutane, kuma irin kalaman da wasu daga cikinsu suka rika yi ya taka muhimiyar rawa wajen  haifar da tunzura al'ummar waɗannan jihohin.

Hakazalika kalaman gwamnatocin yankunan yasa suke ganin kamar jagororinsu na goya musu baya, wanda hakan yaa suka ɗauki wannan mataki na doka a hannun su, inji shugaban Majalisar Dattawa ta ksa.

Ya ƙara da cewa Majalisar Dattawan ta yi muhawara dangane da wannan al'amari bayan kammala hutunta, sannan ta yi tur da Allah wadai da abin da wasu shugabanni na siyasa ke yi na kalaman tunzura al'umma batare da laakari da irin halin da ake ciki akasa n rashin cikakken tsaro wanda dole gwamnatin jiha nada kalan nata gudumuwar don tabbatar da tsaron dukiya da rayuwar al'ummar kasa.