Shugabannin Jam'iyyar PDP sun gana da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan dan fahimtar juna


Shugabannin babbar jam'iyyar adawar Najeriya PDP sun gana da tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan don fahimtar ko da gaske ne ya na shirin sauya sheka zuwa APC.

Tsohon shugaban majalisar dattawa najeriya Bukola Saraki ya jagoranci tawagar sulhu ta PDP zuwa gidan Jonathan a Abuja inda su ka tattauna.

Wannan na faruwa ne daidai lokacin da a ke samun raɗe-raɗin jan hankalin Jonathan da wasu ke yi don ya zama ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyar APC a  shekarar 2023 ya karba daga hannun shugaba Buhari.

Ganawar da ta samu halartar wasu  daga cikin tsoffin gwamnonin PDP, Saraki ya ce an samu nasara don Jonathan ya ce zai cigaba da marawa jam'iyar PDP baya.

Yahaya Turba