Siyasa ce tasa gwamnatin kano dakatar dani cewar Sheik Abduljabbar Nasir Kabara

 


Sheik AbdulJabbar Sheikh Nasir Kabara ya bayyana dakatarwar da gwamanatin Jihar Kano  ta yi masa daga yin wa'azi da rufe masallacinsa da cewa "zalunci ne".shehin Malamin ya faɗa wa wakilin BBC cewa duk da ita gwamnati da kanta, ta bakin kwamishinan Ilimi na jihar kano  ta tabbatar da abin da ake yi masa da cewa zalunci ne, domin  ta dakatar da shi ba tare da ba shi damar cewa komai ba ko kuma ta bukaci ya kare kare kansa ba.

Sheik Abduljabbar yayi  wannan kalami ne biyo bayan rufe makarantarsa da masallacinsa da gwamantin Kano ta sanar da yi a ranar Laraba tare da haramta saka karatunsa a kafafen sada zumunta da na yaɗa labarai a jihar.

Shehin malamin ya ce taron da ya gudanar a makon jiya na daga cikin dalilan da ya sa gwamnatin ta ɗauki wannan tsatsauran matakin, ganin cewar duk yunƙurin hana taron ya ci tura.

Kwamishinan ilimi ya raddi da cewa ana zalunci Sheik Abduljabbar wanda hakan ta sa Sheik  cewa matsyaina na wanda ba kowan kowa ba, kamar kwamishinan ilimi ya ce ana zaluntar Abduljabbar, ai ya isa raddi ga gwamnati cewa abin da ta yi zalunci ne.

"Kuma ta yi wannan kalaman ne kan abin da waɗannan azzaluman da suka tabbata cewa su azzalumai ne, sun sauka daga kan layin ilimi suna amfani da siyasa da gwamnati wajen cimma wani burin su wadda suka kasa cimmawa a ilimance sai da suka yi amfani da gwamnati a siyasance