Taƙaitaccen Tarihin Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Kashi Na Ɗaya 1

Wane ne Ahmadu Bello Sardaunan? 


An haifi marigayi Sir Ahmadu Bello a garin Raɓah dake cikin lardin Sakkwato a shekara ta 1910 ,kuma dan sarauta ne jinin Mujaddadi shehu Usmanu ɗan Fodio, wanda ya kafa daular fulani.Da yake shekara 16 da haihuwa bayan ya sami iliminsa na makarantar lardi ta Sakkwato, daga nan sai ya wuce zuwa kwalejin horon malamai ta katsina, inda yayi karatu daga 1926 zuwa 1931. A kwalejen ta Katsina ya riƙe mukamin mai unguwa,kuma yayi kyaftin na yan wasan Fives. Bayan da ya fita a matsayin malamin makaranta, ya koyar a makaranatr Middile ta Sakkwato daga 1931 zuwa 1938.Daga nan ne kuma aka nada shi Sardaunan Sakkwato,watau mai baiwa sarkin musulmi shawara akan harkokin siyasa.

Daga nan sai aka danka masa shugabancin yakin gabas na Sakkwato,wato Gusau inda hakimai goma sha hudu daga cikin arba’in da bakwai na Sakkwato ke karkashinsa. A cikin shekaran 1944 ya koma Sakkwato a mukamin baban mai bayar da shawara ga sarkin musulmi.

Nan zamu tsaya cikin takaitaccen tarihin marigayi Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto.