Ƙwallon ƙafa: Liverpool da Manchester da wasu manyan kilob a Ingila suna rubutun Ezri Konsa

Ƙungiyar Liverpool na duba yiwuwar ɗauko ɗan wasa Ezri Konsa, ɗan wasan baya na Aston Villa mai shekara 23, nan da karshen wannan kakar wasan. Kazalika itama ƙungiyar Liverpool, da Manchester United, da Manchester City da kuma Tottenham duk suna na sha'awar ɗaukan Mathew Hoppe, dan wasan Schalke mai shekara 19 domin ya buga mu su. Wannan lamarin ya zama na mai rabo ka samu. 

Dan wasan gaba na Paris St-Germain ɗan ƙasar Faransa, Kylian Mbappe ya tabbatar wa kungiyar sa cewa zai yi zamansa tare da ƙungiyar in da ya amince da tsawaita kwantiragin sa har zuwa 2022, lokacin da kwantiragin sa ta yanzu za ta kawo karshe. 

Dan wasan Manchester City da Jamus Ilkay Gundogan mai shekara 30, ya fara tunanin ritaya daga buga kwallo, inda ya sanar cewa manema labarai cewa yana son zama koci ne bayan ya bar kwallon kafa.

BBC Hausa