Yadda zata kaya a kakar gasar bana a nahiyar Turai

Timo  Werner ɗan wasan Chelsea  mai shekara 24 wanda ya gaza zura kwallo ko daya  a wasanni 14 da ya buga a gasar firimiyar Ingila. Sai gashi yana tabbatar da cewa akwai lokaci na zuwa da zai koma ganiyarsa 

fasahar VAR na kawo sauye-sauye saboda zamani, cewar tsohon alkalin wasan gasar firimiya Mark Halsey amma ya buƙaci a tausaya wa alkalan wasan wadanda sun kusa kasa wa saboda gajiya

Stefano Pioli Manajan kulop dinAC Milan ya ce ya dace a ce Zlatan Ibrahimovic, dan wasan gaba mai shekara 39 ya ci gaba da buga wasan sa tare da kungiyar ta Italiya. Wa'adin dan wasan zai ƙare kakar bana. (Sky Sports)

Kocin Tottenham Jose Mourinho ya baiyana cewa sabunta kwantiragin Son Heung-min, dan wasan kungiyar mai shekara 28, wanda wa'adin kwantiragin sa zai kare a 2023, na bukatar hakuri da dabara.

Raunin da ɗan wasan baya na kasar Spaniya Sergio Ramos da ya ke fama da shi na iya jawo jinkirta  sabunta kwantiraginsa a ƙungiyar ta Real Madrid har zuwa lokacin da ya warke, inda wa'adin ɗan wasan mai shekara 34 zai zo  karshe a karshen wannan kakar wasan na bana.

 Roy Hodgson Mai horar da yan wasan Crystal Palace ya na  sa ran kungiyarsa ta ɗauko Wilfried Zaha a karshen wannan kakar wasan, ganin cewa ɗan wasan mai shekara 28 ɗan kasar Ivory Coast na sha'awar buga wasannin gasar Zakarun Turai.

 (Source BBC)