Alexandre Lacazette ɗan wasan Arsenal zai yi awon gaba a kakar bana....

Firaminista Boris Johnson na ƙasar Birtaniya ya  sanar da shirin ƙasar sa na ɗaukar nauyin dukkan gasar Zakarun NahiyarTurai a ƙarshen kakar wasa ta bana  

ƙungiyar West Ham na fatan dauke Tammy Abraham daga Chelsea a karshen wannan kakar wasan. Ɗan wasan gaban mai shekara 23 da wasu 'yan wasa biyu, Edie Nketiah na Arsenal mai shekara 21 da Ivan Toney na Brentford mai shekara 24 ma na cikin jerin ƴan wasan da su ke fatan sayewa. 

Dan wasan baya na Reading Omar Richards mai shekara 23 zai koma Bayern Munich na wa'adin shekara hudu a karshen wannan kakar wasan. 


Dan wasan gaba na Arsenal ɗan ƙasar Faransa, Alexandre Lacazette mai shekara 29 ya dab da yin awon gaba daga ƙungiyar a karshen wannan kakar wasan.