Amon ƙarar harbe-harbe da bindiga a dab da fadar shugaban ƙasar Nijar


Gidan radiyon BBC Hausa sun ruwaito a Shafin su na intanet cewa.rahotanni daga Jamhuriyyar Nijar a safiyar yau na cewa an ji ƙarar harbe harben bindiga a kusa da fadar shugaban ƙasar da ke birnin Yamai.

Zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani dangane da wannan al'amarin, inda wasu rahotanni ke nuna cewa kamar al'amura sun dan daidaita 

Hakazalika rahotannin da muke samu sun bayyana cewa wasu ofisoshin jakadancin ƙasashen waje dake birnin na Yamai sun yi kira ga ma'aikatansu da su zauna a gida kada su zo aiki.

Sai dai har yanzu Gidan rediyon ƙasar ya Nijar mallakar gwamnati dake birnin na Yamai na ci gaba da watsa shirye shiryensa ba tare da wata tangarda ba.

Ku ci gaba da kasancewa da mu don samun cikakkun rahotannin da ƙarin bayani kan halin da ake ciki.