Ƙungiyar Arsenal za ta chanza Alexander Lacazatte da Ibrahim konate

Ƙungiyar Arsenal ce kan gaba cikin kungiyoyin da ke yunkurin daukar dan wasan RB Leipzig Ibrahim Konate mai shekara 21 a kakar wasan Bana.'


Konate na daga cikin ƴan wasa shida da Arsenal suka  sawa a karon zuƙa yayin da kungiyar ke fatan sayar da ɗan wasan gabanta ɗan kasar Faransa Alexandre Lacazette mai shekara 29.

Kocin  ƙungiyar Manchester City Pep Guardiola ya kara nuna sha'awar sa kan ɗan wasan Aston Villa mai shekara 25 Jack Grealish, sai dai ita kungiyar da ke jan ragamar gasar Premier ta fi damuwa da  ta dauki dan wasan tsakiya na matsawa gaba da kuma mai bi ta bangaren hagu a ƙungiyar.

Ɗan wasan tsakiya na Manchester United ɗan kasar Portugal Bruno Fernandes mai shekara 26, ya shirya tsaf domin tsawaita kwataraginsa  a ƙungiyar wanda hakan zai sanya a ninka masa kudin da ya ke karɓa  a mako zuwa fan 200,000 

BBC