Asalin taƙaitaccen Jawabin,Yadda ranar 8 ga watan Maris na kowacce shekara ta zama, "Ranar Mata" ta duniya

Kowacce Ranar 8 ga watan Maris ne. Ranar Mata ta Duniya wanda Clara ta bullo da shawara a kai ko da yake ba ta da takamaimen rana da aka tsayar a lokacin

Sai Wannan rana ba ta kasance a hukumance ba har sai lokacin da wata zanga-zangar da akayi lokacin yaki a shekarar 1917 lokacin da matan kasar Russia suka bukaci ''biredi da zaman lafiya'' - 

Daga wannan rana kwanaki hudu da fara yajin aikin matan, aka tilasta wa shugaban ya sauka daga mukaminsa kana gwamnati ta amince wa mata samun 'yancin kada kuri'a a wancan lokacin.

Ranar Lahadi 23 ga watan Fabrairu ne  matan suka fara gudanar da yajin aikin kan tsarin kalandar kwanan wata ta Julian da kasar Russia ke amfani da ita a wancan lokacin.

Wanda a yanzu wannan rana a kan tsarin kalandar Gregorian ne ta kasance ranar 8 ga watan Maris- shi yasa a yau ake wannan bikin a kowacce rana mai kamar ta yau

BBC Hausa