Search Items

Ƙasar Amurka ta zargi Najeriya da yin rufa-rufa a kan kisan almajiran Malam Ibrahim El-zakzaky

Wani rahoton da Amurka ta fitar a kan batun kare haƙƙin ɗan adam a Najeriya cikin shekara ta 2020 ya ce har yanzu babu wani ƙarin bayani kan binciken gwamnatin tarayya ko kama wasu da hannu a kashe-kashen da sojojin ƙasar suka yi wa mabiya  ƙungiyar Shi'a ta Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Kasar Amurka ta ce kamata ya yi a ce zuwa yanzu Najeriya na da wani ƙarin bayani da za ta iya yi wa duniya a kan zargin da ake yi wa dakarun sojin ƙasar na kisan almajiran Zakzaky kimanin 347, da kuma binne su a manyan kaburbura domin boye abin da aka aikata a idon duniya.

Hakazalika rahoton ya kuma yi dogon sharhi game da take haƙƙin ɗan adam a shekara ta 2020, kama daga kan wanda ake samu a tsakanin jami'an tsaron Nijeriya da kuma kungiyoyin ƴan tayar da ƙayar bayaharma da wasu da akewa lakabi da ƴan tsageru musamman a kudancin Najeriya

A wasu bangarorin kuma shugaban ya kalli ci gaban da aka samu kan kokarin kare hakkin ɗan adam, ciki har da hukuncin shekara 55 a gidan maza da aka yanke wa wani soja a watan Agusta da ta shuɗe bayan kotun soji ta same shi da laifin aikata kisan kai a jihar Zamfara, da ke arewa maso yammacin kasar.

Haka ma ya zargi kungiyar Boko Haram da ISWAP da sace-sacen mutane masu yawa a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa. ya kuma zargi jami'an tsaro da tsare mutane ba bisa ka'ida ba, da cin zarafin ɗan adam da azabtar da waɗanda ake zargi, inda ya ce akwai kotunan shari'a a jihohi 12 da Abuja, waɗanda suna iya yanke hukuncin bulala ko sare hannu ko ma jefewa.

Wani batu kuma da rahoton ya yi duba a kai shi ne na yawan cunkoson ɗaurarru mutane a gidajen yarin Najeriya, da kuma yadda ake ɗaukar munanan dabi'u a cikinsu.

Ya kuma nuna damuwa a kan yadda a wasu gidajen yarin ma babu wani tsari na kula da mata masu ɗauke da juna biyu, baya ga matsalar rashin isashshen abinci da ruwan sha da mutanen ke fama da ita.

Sa'annan rahoton ya ce duk da ɓangaren shari'a na da ikon cin gashin kanta a Najeriya, akan samu ɓangaren zartaswa da yi masa katsalandan domin cimma wasu manufofi na kashin kai, abin da ya saba wa doka.

Source: BBC Hausa