Search Items

Chelsea da Manchester suna karakaina a kan tsohon ɗan wasan Chelsea Lukaku


Ƙungiyar Chelsea na duba yiwuwar sake daukar ɗan wasan Belgium kuma tsohon ɗan wasan Kungiyar Romelu Lukaku, mai shekara 27, idan ta gaza daukar ɗan wasan Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 20, a bazarar nan.

Hakazalika itama ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City tana son daukar Lukaku, wanda ya zura kwallo 59 a wasanni 85 da ya murza a Inter Milan a kakar bana.


Borussia Dortmund ta sanya kudi kan Haaland ga masu son daukarsa a bazarar nan inda ta ce duk kungiyar da ke bukatar dan wasan za ta ajiye akalla £154m. (ESPN)

Jaridar sun ta wallafa cewa Sadio Mane ɗan wasan Senegal mai shekara 28, ya bayyana muradin sa cewa zai ci gaba da zama a Liverpool - ko da kuwa kungiyar da Jurgen Klopp yake jagoranta ba ta samu gurbin zuwa gasar Zakarun Turai na kakar wasa mai zuwa ba.