Cristiano Ronaldo; Da alamun Ƙungiyar Arsenal na zawarcin Babban ɗan wasa:

Jaridar Liverpool Echo. Ta wallafa cewa Liverpool ta ce ba ta san da wata yarjejeniya ba da ta kulla da Barcelona cewar za ta dauki dan wasan tsakiya Georginio Wijnaldum, mai shekara 30 ba, kafin ta sayi dan wasan na kasar Holland. 


Kociyan ƙungiyar Arsenal dake Ingila Mikel Arteta ya ce Martin Odegaard shi ne jagoran 'yan wasan kungiyar, kuma ya nuna aniyarsu ta daukar ɗan wasan na real Madrid ɗan Norway mai shekara 22 ya zauna dindindin.a kulop ɗin.

Juventus ta ce a shirye take ta ba wa Everton 'yan wasa har da kudi domin dawo da tsohon dan wasan ta na gaba ɗan ƙasar Italiya Moise Kean mai shekara 21, kamar yadda Tutto Juve ta ruwaito daga Teamtalk.

Ita kuwa kungiyar Crystal Palace na harin sayen ɗan wasan baya ne na Juventus, ɗan ƙasar Romania Radu Dragusin mai shekara 19. Kamar yadda jaridar Sun ta ruwaito.