Search Items

Dan shugaban kasa Muhammadu Buhari zai auri Ƴar Sarkin Bichi


Gidan radiyon BBC Hausa sun ruwaito cewa Yusuf Buhari, ɗan  shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai auri Zarah Nasir Ado Bayero, 'yar gidan Sarkin Bichi, bayan karamar sallah mai zuwa.

Wata majiya mai kusanci da fadar masarautar Bichin ta tabbatar wa BBC cewa ɓangarorin biyu sun haɗu sun tattaunawa kan soyayyar da ke tsakanin matasan biyu Yusuf da zahara.

Kazalika majiyar, wadda ba ta so a ambaci sunata, ta ce ɓangaren shugaban Najeriya ne ya tafi wurin iyalan marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero domin neman auren Zarah Nasir Bayero.

Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa bangarorin biyu sun amince tare da tsayar da lokacin bikin zuwa bayan sallah, ta yiwu bayan sallar azumi ko kuma layya," in ji majiyar tamu.

Wasu majiyoyi sun tabbatar mana cewa matasan biyu sun haɗu da juna ne a ƙasar Ingila inda Yusuf ya kammala karatunsa na digiri yayin da ita kuma Zarah har yanzu tana ci gaba da nata karatun a chan ƙasar Ingila.

Ta bayyana cewa an so a ɗaura auren tun watannin da suka gabata amma hakan bai yiwuwa ba saboda mahaifiyar Yusuf, Aisha Buhari, tana birnin Dubai, inda ta kwashe watanni da dama kafin ta koma Najeriya.

A watan Fabrairun 2018, fadar shugaban Najeriya ta ƙaryata labarin da ke cewa ɗan shugaban ƙasar Yusuf Buhari ya rasu.

Wasu shafukan intanet ne suka wallafa labarin da ke cewa ɗan gidan shugaban ƙasar ya rasu sakamakon raunukan da ya ji bayan hatsarin da ya yi a kan wani babur na alfarma a watan Disambar 2017 a Abuja.

A watan Maris ya komo Najeriya kuma tun daga lokacin ba a sake jin ɗuriyar sa sosai Yusuf ne ɗan Aisha Buhari na uku da zai yi aure tun da Muhammadu Buhari ya zama shugaban ƙasa a shekarar 2015 zuwa yanzu.