Dr. Kabir Adamu: Shawarar ɗaukan matasa Miliyan 50 aikin soja tunanin ya saɓa wa hankali


Jagora a jam'iyar a APC a Najeriya Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya yi kira ga shugaban kasa da a ɗauki matasa miliyan 50 aikin soja, domin shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi yankunan ƙasar nan baki ɗaya.

Bola Tinubu ya bada wannan shawarar ne yayin ake taron taya shi murnar zagayowar shekarun haihuwarsa da aka saba gudanarwa duk shekara, wanda a wannan karon aka yi a jihar Kano dake arewacin Nigeriya

Da yake nuna damuwar sa kan yadda yawancin matasan ƙasar ke fama da rashin aikin yi, Ahmad Tinubu ya ce babban abin da yanzu ya kamata gwamnatoci su maida hankali a kai shine gina rayuwar ɗan adam, ciki kuwa har da samar wa matasa ayyukan yi a faɗin ƙasar.

Sai dai wannan furuci da  Tinubu ya yi sun janyo muhawa a tsakanin wasu ƴan kasar da kuma masu fashin baki kan al'amuran yau da kullum da suka shafi tsaro.

Dr Kabiru Adamu na kamfanin Beacon Consulting da ke nazarin tsaro a Najeriya da yankin Sahel ya ce babu yadda za a yi ƙasa irin Najeriya, wadda yawan al`umar bai dara na kasashe irin su China Indiya ba ta tara sojojin da suka kai miliyon biyar ba ballantana miliyon hamsin, yana jaddada cewa su ma masu yawan al`ummar ba su yi haka ba, saboda adadin ya saba wa hankali.

BBC Hausa