Gwamnatin jihar Kano tace ba da yawun ta aka dakatar da Muƙabula da AbdulJabbar ba.


Gwamnatin jihar Kano ta bayyana Matsayinta da hukuncin da wata kotun majistre a jihar  Kano ta yanke na dakatar da yin muƙabala, wato zaman tattaunawa da fitaccen malamin addinin musuluncin nan dake jihar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

JiyaJumma'a ne kotun ta yanke wannan hukunci, kimanin kasa da sa'o'i 48 da za'a fara gudanar da muƙabalar da aka jima ana jiran ranar, duk da cewa gwamnatin jihar Kano ta ce bada yawun ta aka shigar da kara ba amma ta gamsu da hukuncin.

Cikin Hukuncin kotun ta buƙaci a tsaya a kan hukuncin da kotun ta yanke tun a ranar 8 ga watan Fabrairu, wanda ta yi umurnin haramtawa Sheikh Abduljabbar yin wa'azi da karantarwa a faɗin jihar ta Kano.

kwamishinan watsa labarai na Kano Muhammadu Garba, a zantawar sa da gidan rediyon BBC ya ce bayan tattaunawa da gwamnati ta yi da ma'aikatar shari'a, sun gamsu da wannan hukunci, don haka an dakatar da yin muƙabalar da aka shirya gudanarwa a ranar Lahadin nan.

Sai dai daga ɓangaren AbdulJabbarNasir wani daga cikin lauyoyin dake kare Sheikh Abduljabbar a shari'ar Barista Rabiu Shu'aibu Abdullahi, ya ce su a iya saninsu wannan zama yana nan daram, domin babu wani takarda ko wani waje da kotun ta fito ƙarara ta ce ta hana yin Muƙabala a sani su.

Barista Rabi'u ya ce a fahimtar su da wannan hukunci shine kotu ta ce a ci gaba da aiki da hukuncin da ta yanke na ranar 8 ga watan Fabrairu. na cewa ta hana Malam Abduljabbar yin wa'azi da kuma furta kalaman tunzuri, da rufe masallacinsa da cibiyarsa, babu wani waje da tace kada a yi muƙabalar da aka shirya.

Kazalika ya ƙara da cewa kwata kwata takardar hukuncin da kotu ta yanke bashi da alaka da yin muƙabalar, ballantana a ce za a fasa yin zama.