Joan Laporta.Barcelona tayi alkawarin lallashin Lionel Messi ya ci gaba da zama a kungiyar.

Joan Laporta - mutumin da ya soma wa'adi na biyu na shugabancin Barcelona - ya ce zai yi kokari ya rarrashi dan wasan Argentina Lionel Messi ya ci gaba da zama a kungiyar. Dan wasan, mai shekara 33, wanda zai sake kafa sabon tarihi a Barcelona idan ya buga wasan da za su yi na gaba, kwangilarsa za ta kare a karshen kakar wasan bana. Mohamed Elneny dan wasan Arsenal da Masar  Elneny, mai shekara 28, yana son ya sanya hannu kan sabon kwantaragi kuma ya ce bai yi tunanin cewa zamansa ya kare a kungiyar  ba lokacin da ya tafi zaman aro a Besiktas a kakar wasan da ta gabata.

Kungiyar Borussia Dortmund na son daukar dan wasan Liverpool da Belgium Divock Origi,, kuma tana iya neman daukarsa a bazara. Origi, wanda ya zura kwallo a wasan karshe na gasar Zakarun Turai a kakar wasan bara waccan, za a iya sayar da shi a kan £12m. 

Tsohon dan wasan Arsenal da Ingila Kieran Gibbs, mai shekara 31, ya amince ya tafi Inter Miami a karshen kakar wasan da muke ciki inda ya yarda da yarjejeniyar shekara biyu da rabi da zarar kwangilarsa ta kare a kungiyar  West Brom take Ingila. 

Dan wasan tsakiyar Netherlands Donny van de Beek, mai shekara 23, ya ce ya ji dadin "kaunar" da aka nuna masa a Manchester United amma yana so ya soma buga wasanni da dama, a cewar kocin Netherlands Ronald de Boer. 

BBC /football insider