Juventus zata tsawaita kwantiragin Cristiano Ronaldo


Juventus za ta duba yiyuwar tsawaita kwantiragin Cristiano Ronaldo  Wannan sanarwar ta fito ne daga daraktan wasanni na kungiyar Fabio Paratici 

Ƙungiyar Barcelona ta bai wa ɗan wasan gaba na Argentina Sergio Aguero mai shekara 32 kwantiragi wanda kwantiraginsa da ƙungiyar Manchester City zai zo dab ƙarshe 

Real Madrid za ta saurari tayi kan ɗan wasanta na baya Rapheal Varane a kakar wasan nan. Rahotanni na cewa ɗan wasan na Faransa mai shekara 27 ya nuna sha'awa a wani mataki na son shiga gasar Premier ta Ingila 


Chelsea na iya sayar da ɗan wasan gaba na Jamus Timo Werner a wannan kakar wasan shekara ɗaya bayan da ɗan wasan mai shekara 25 ya bar ƙungiyar sa ta RB Leipzig kan kuɗi £54m.