Lionel Messi da Ronaldo sun sake Kafa tarihi a duniyar kwallon kafa a nahiyar Turai
Lionel Messi ya yi murnar kafa tarihin buga wasanni 768 a Barcelona tare da zura kwallaye biyu a wasan da kungiyar ta doke Real Sociedad da ci 6-1 a gasar La Liga a ranar Lahadi da ta gabata.Yanzu haka Messi ya sha gaban tsohon dan wasan tsakiya na Barcelona wato Xavi wajen yawan wasanni a Camp Nou, inda ya ba shi tazarar wasa guda kawai.
Ɗan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa na Juventus, Cristiano Ronaldo, ya sake nuna bajinta a karawar tawagarsa da kungiyar Spezia a ranar Talata karkashin gasar Serie A ta Italiya inda ya ingiza tawagar tasa ta yi nasara da kwallaye uku da nema.
Dan wasan na Portugal da ya taba buga wasa a kungiyoyin Manchester United da Real Madrid bajintar da ya sake nunawa a wannan kaka, ta mayar da shi dan wasa daya tilo da ya iya zura kwallaye 20 ko fiye cikin kowacce kakar wasa a manyan gasannin Turai guda biyar cikin shekaru 12 da suka gabata.