Mikel Obi ya kasance na ɗaya cikin jerin tajiran ƴan kwallo a Najeriya

Mikel Obi ɗan wasan ƙwallon ƙafa mai shekaru 33 ya ba Naira biliyan 23 baya. ‘Dan wasan tsakiyar dake kwallon sa a ƙungiyar Stoke City ya buga wa Tianjin TEDA bayan ya bar Chelsea a 2017.

‘Dan wasan ya kasance na biyu a jerin attajiran yan kwallon tsohon ‘dan wasan Inter Milan da Newcastle, Obafemi Akinwunmi Martins wanda ya mallaki Naira biliyan 14.

Obafemi Martins wanda aka rikayi wa lakabi da Obagoal ya na gaban Odion Jude Ighalo cikin jerin tajiran.

Rahotan BBC ta ce ‘dan wasan gaban na Wuhan Zall ya mallaki fiye da Dala miliyan 25 da kuma manyan gidaje a Legas da ƙasar Italiya da dirka-dirkan motoci na alfarma.