Search Items

Miyagun aiyuka baza su ƙare a Najeriya ba har sai an Samar Wa matasa aikin yi a fadin ƙasar


Babban jigo cikin manyan ƴan Jam'iya Asiwaju Bola Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ya ce har yanzu tattalin arzikin Najeriya yana da rauni duk da cewa kasar ta fice daga durkushewar tattalin arzikia kwanakin baya.

Tinubu ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi a taron tunawa da sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, da aka yi a Kaduna ranar Asabar ɗin nan data gabata.

Hukumar kididdiga ta kasar a watan Fabarairun da ya gabata ta sanar cewa arzikin da kasar ta ke samar wa cikin gida ya karu da kashi 0.11 a karshen wata hudu na shekarar 2020.

A cewar hukumar ta NBS, ci gaban ya nuna cewa tattalin arzikin kasar ya farfado daga koma bayan da ya samu.

Sai dai a jawabin da ya yi lokacin da ya gabatar da wata takarda mai taken "Rage yawan kuɗin da ake kashewa kan shugabanci don ci gaban kasa da matasa a arewacin Najeriya bayan annobar korona", Tinubu ya ce har yanzu da sauran rina a kaba.

Tsohon gwamnan jihar Legos ya ce duk da matakan da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta dauka, har yanzu tattalin arziki kasar yana da rauni saboda akwai mutane da dama da ba su da ayyukan yi a ƙasa.

Ya yinda kasar ta ke fuskantar kalubalen tattalin arziki sai aka samu bullar annobar korona wadda ta shafi tattalin arzikin duniya baki daya ciki har da Najeriya a cewar sa.

Sai dai ya jadadda bukatar ganin cewa an zaftare yawan kuɗaɗen da ake kashe wa jami'an gwamnati masu madafan ikon domin ƴan Najerya su amfana daga tattalin arzikin kasarsu.

Da yake Magana game da karuwar tashin hankali musamman a rewacin Najeriya, Tinubu ya ce kasar ba za ta iya shawo kan matsalar ma su aikata miyagun laifuka ba, da kuma matasa ma su tada husuma idan ba ta samar mu su da guraben ayyukan yi ba.

BBC Hausa