Search Items

Rundunar ƴan sandan Najeriya sunyi babban kamu
Dakarun 'yan sanda kwararru daga sashin binciken manyan laifuka da neman bayan sirrina tsaro na rundinar 'yan sandan Nigeria, Force Intelligence Bureau (FIB) Abuja, tare da hadin gwiwar 'yan sandan jihar Kaduna Operation Yaki sunyi babban kamu...

Jami'an 'yan sandan sun bi diddigin wasu manyan barayi wadanda suke tafiya a cikin mota samfurin High-Lander mai dauke da rijista LGT 582 JL a jejin Saminaka dake yankin jihar Kaduna, barayin da suka lura 'yan sanda na binsu sai suka bude wuta, daga nan aka fara musayen wuta, wasu daga cikin barayin suka fita daga motar suka gudu

'Yan sandan sun samu nasaran kama mutum biyu, daya sunansa James Dungs shekarunsa 30 ya fito daga garin Jos jihar Pilato, dayan barawon sunansa Oga Joseph, shima daga garin Jos jihar Pilato, sai kuma dayan barawon mai suna Justine Oraduen wanda ya mutu sakamakon harbi

'Yan sandan sun duba motocin barayin, sun samu samfurin bindigar AK47 guda 8 kirar hannu, sannan da karamar bindiga Pistol kirar hannu guda 1, Magazine na AK47 guda 11 da harsashin bindigar AK47 guda 50

Barayin sun tabbatar wa 'yan sanda cewa suna kan hanyar su ne zasu raba makamin wanda aka kera da hannu zuwa ga barayin da suke ta'addanci a jihohin Niger, Kaduna, Katsina da Zamfara

Abinda ya ja hankalina shine yadda aka fara kera samfurin bindigar AK47 kirar hannu a cikin garin Jos ana rabawa barayi, wato ko da an toshe hanyar shigowa da bindigogi daga kasashen waje yanzu akwai masu kera wa a cikin gida, hakika wannan ba karamin barazana bane wa harkan tsaron Nigeria

Kuma abin takaici sai 'yan sanda sun sadaukar da rayuwarsu sun hana idon su bacci, sun sha wahala sun kama manyan barayi, idan an kaisu kotu don su fuskanci hukunci, wasu Lauyoyi kuma jira suke a biyasu makudan kudi su kubutar da barayin.


Source Dw Hausa