Rundunar Ƴan Sandan Najeriya ta kafa gidan rediyon ta na musamman


Gidan radiyon BBC sun ruwaito cewa Rundunar ƴan sandan Najeriya ta kaddamar da gidan rediyo na kanta da zummar inganta dangantakar da ke tsakaninta da jama'ar Najeriya Babban sufeton rund ƴan sandan Mohammed Adamu, wanda shi ya kaddamar da gidan rediyon mai suna Nigeria Police 99.1FM Radio ranar Laraba a Abuja, ya ce gidan rediyon zai taimaka wajen rage aikata laifuka ta hanyar watsa labarai game da yadda za a kama masu laifuka da ma hana aikata wasu miyagun laifukan.

"Tuni gidan rediyon The Nigeria Police 99.1FM ya soma gudanar da aiki na gwaji Wanda a turance ake kira da Test Transmission kamar yadda dokar hukumar kula da kafafen watsa labarai ta tanadar. 

Gidan rediyon zai zama wata hanya da rundunar ƴan sandan Najeriya za ta tattauna tare da wayar da kai da kuma ilimantar da ƴan kasar game da ayyukanta da kuma sauran lamuran da suka shafi harkokin tsaro," a cewar babban sifeton ƴan sandan Mohammed Adamu.

Ya kara da cewa gidan rediyon zai riƙa gabatar da shiri na kai-tsaye da ƴan ƙasar za su rika kiran waya game da yanayin tsari a yankunasu musamman kan yadda za su gano masu aikata laifuka da bayar da rahoto a kansu ta yadda jami'an tsaro za su yi saurin kai musu dauki.

Twitter