Search Items

Sanata Abdullahi Adamu ya gano yadda Gwamnati zata magance rikicin Makiyaya da Manoma a faɗin ƙasar nan


Daya daga cikin dattawan a arewacin Najeriya kuma ɗan majalisar dattawa daga jihar Nassarawa Sanata mai wakilta shiyyar Nasarawa ta yamma Sen.Abdullahi Adamu, ya ce ana ƙoƙarin fakewa da sunan hare haren da ake zargin makiyaya na kaiwa wasu jihohin ƙasar domin raba kan al'ummar yankunan a arewacin ƙasar nan..

Wannan batun ya zone Yayin wata hira da wakilin BBC Sanata Abdullahi Adamu, ya ce rikicin makiyaya ya samo asali ne sakamakon cinye hanyoyi ko burtalan da suke bi, da kuma dazukan da aka keɓe musamman don kiwo, sannan aka ƙi samar da wani shiri don ganin sun gudanar da harkokinsu na kiwon.

Hakazalika ya ce ana neman dalili ne kawai domin bata sunan makiyayi don a la'ance su, ana maganar kiwo wake maganar kudu ?, ai kowa ya san kiwo a arewa yake, don haka wuta ce ake kunnowa domin ganin an raba kan a;'ummar arewacin najeriya a cewar Sanata Abdullahi Adamu.

Da ƙarshe yayi kira ga Gwamnati da cewar matsawar ana son kawo ƙarshen wannan matsala, ya zama dole ne gwamnati ta fahimci haɗarin da ke tattare da bari a rika yin kiwo barkatai, alabashi idan ta fahimci haka sai ta samarwa makiyayan wata hanya da za su rika gudanar da harkokinsu.