Shugaba Buhari ya baiwa Jami'an tsaro Makonin 6 su kawo ƙarshen matsalar Tsaro

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnati ba za ta yi sassauci ga masu ɗaukar bindiga suna kashe-kashe ba kuma ya jaddada umarnin da ya bayar a baya-bayan nan cewa duk wani wanda ba jami'in tsaro ba aka kama shi da manyan makamai irin bindigar nan ta AK 47 a harbe shi.

Shugaban ƙasa  ya yi mamakin duk da cewa ba a daɗe da sake bude iyakokin ƙasar ba amma yan bindigar ba sa rashin makamai.

Wannan dalilin haka ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya baiwa sababbin shugabannin tsaro daya naɗa a ƴan kwanakin da suka shuɗe wa'adin mako shida ya ga sauyi a ƙasa game da tsaron rayuka da dukiyar al'umma.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba zai yiwu damina ta faɗi mutane ba za su iya shiga gona su yi noma ba.

Gamayyar Sarakunanan gargajiyar ƙsar ne suka kai kukan su ga shugaban game da taɓarɓarewar tsaro a ƙasar, sai dai wasu na ganin jami'an tsaro za su fuskanci ƙalubale musamman idan aka dubi cewa wannan yaƙi ne na sari ka noƙe ba'a fitowa sarari.